Wednesday, 25 October 2017
DA DUMIDUMINSA An Kashe Matar Shekau A Wani Hari Da Sojoji Suka Kaiwa 'Yan Boko Haram A Borno

Home DA DUMIDUMINSA An Kashe Matar Shekau A Wani Hari Da Sojoji Suka Kaiwa 'Yan Boko Haram A Borno
Ku Tura A Social Media

Rundunar sojojin saman Nijeriya a yau Laraba ta sanar da cewa tana da tabbacin cewa matar shugaban Boko Haram, Malam Firdausi tana daga cikin wadanda suka mutu a yayin harin sama da sojoji suka kai mafakar 'yan Boko Haram din dake yankin Durwawa a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Daraktan yada labarai na rundunar sojojin saman, Air Commondore Olatokunbo Adesanya, shi ya tabbatar da hakan a yau a Abuja.

Kamar yadda Adesanya ya bayyana, Firdausi ta wakilici mijinta Shekau ne a wani taro na 'yan ta'addan a wurin da sojojin suka kai farmakin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: