Saturday, 14 October 2017
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Shariff (momo)

Home Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Shariff (momo)
Ku Tura A Social Media
Daga Sa'idu Bahaushe

Kodayake ban sani ba ko ka taba yin karatun aikin Jarida ko kuma yin aiki a wata kafar yada labarai ba kafin zuwanka tashar Talabijin ta Arewa24 kana gabatar da Shirin Kudin Kannywood.Amma katobar tambaya don neman suna da cewa ka kware da sakin baki ya hambarar da kai ga yin tambaya game da Addinin Allah a wajen da ba muhallinsa ba tunda shirin nishadi ne a cikin kayanka na sanyi ga Jaruma Umma Shehu.

Wauta da rashin sanin makamar kwadagonka sun sanya ka yin shirme ga Addinin da ba ka isa ka bata ba ko ita Umma ta bata ba.Na daya Addinni ya kyamaci kure don tozarci,kamar yadda ya shimfida ka'idar kare mutuncin Musulmi(Momoh a duba Arba'unan Nawwawi)!Ina fada maka ne don ka mai da maganar nishadi ta Addini alhali babu kira bai kamata mu ga gawayi ba,ballantana abin da ya ci shi!

Ga wasu 'Yan tambayoyi don Allah.Ko meye burgewa idan ka bayyanawa Musulmai da wadanda ba Musulmai ba cewa wani Musulmi bai fahimci komai a cikin Addininsa ba?
Ko a tunaninka gyara ne don gaba ko kure ne da tozarci ka yi?

Ko a matsayin ka na Dan Fim nasara ce idan ka wulakanta Abokiyar Sana'arka da ta fiddo ka tare da yi maka Riga da Wando?

A matsayin na Babban mai gabatar wa ko me ka jawo wa wurin aikinku da irin wannan shibircin aikin da bai kai ko da darajar ruwan Aski ba?
A ganinka yadda kake hira da su da irin wannan salon kana dariya,nan gaba da bayyanar haka wasu za su ci gaba da halartar shirin naka,to ci gaba ko aikin mai ginin rijiya?

Da a ce kokarinka na mai kwazo ne a harkar Addini da bakinka bai sanya ka bar shirin ya fita ba tunda za a Iya tace shi!

An ta jin Hujjojin buge na cewa ita ta tado maganar to kai aikin me kake yi a matsayin(anchor) watau Madugun gabatarwa?Kai sai ka zama rakumi marar akala bayan ka yi takalarka!
Zai kyautu hukumomin tashar su taka maka birkin karfe don ka San me za ka rika fada lura da sukar da tashar ke Sha kan bata tarbiyya daga wadanda ke caccaka!

Bai kamaci mai hankali ya Yanke mata hukunci da cin mutuncinka ba lura da ba-zata,kamar kuma yadda ya kamata kowa ya fahimci cewa ka nufi daji.
Amma tunda da Addini ka ke, to kazo da wuta maishi nada ruwa.!

Mun dauko daga shafin instagram na @kannywoodexclusive

Share this


Author: verified_user

1 comment:

  1. Hmm ina ganin bai kama ce ka da irin wannan tambayoyi ba kuma ina mai baka shawara da ka gayyaci #bello muhammad bello domin ku tattauna domin yana son irin wadannan tambayoyin .

    ReplyDelete