Thursday, 19 October 2017
BBC HAUSA Baku Yiwa Kasar Saudiyya Adalci Ba!!!

Home BBC HAUSA Baku Yiwa Kasar Saudiyya Adalci Ba!!!
Ku Tura A Social Media
BBC HAUSA BAKU YIWA KASAR SAUDIYYA ADALCI BA.

Ba Shakka saka Kasurgumin Dan Bidi'a Ibrahim Maqari da BBC Hausa sukayi domin yayi fashin baki akan matakin Kasar Saudiyya na kafa cibiyar Hadisan Manzon Allah a Birnin Madina wannan rashin adalci ne.

Dafarko dai Ibrahim Maqari bai taba zama Kasar Saudiyya ba, iyakacin sa ya shigo yayi Umrah ko Hajji, saboda haka ba shida ilimi akan Kasar Saudiyya domin labari kawai yake ji.

Na biyu Ibrahim Maqari Kasargumin Dan Bidi'a ne wanda yake matukar Kiyayya da Manhajin Ahlissunnah Waljama'a da Kasar Saudiyya ta ginu akai, saboda haka ba yadda za'ayi ya yiwa Saudiyya adalci saboda Kiyayya da Kasar dake cikin zuciyar sa.

Akwai Malamai Ahlissunnah wadanda suka zauna Saudiyya shekara da shekaru, su ya kamata a kira a tattauna dasu.

Maganar Maqari ta yau da safe Cike take da rashin adalci, Gwamnatin Saudiyya bata koyar da kowa Ta'addanci ba, in muna son mu gano hakan mu dubi Dalibai da sukayi karatu Kasar Saudiyya shin mun taba Jin su cikin Kungiyoyin yan ta'adda? Da ace Saudiyya ke Koyar da ta'addanci da Dole cikin Shekarau fiyeda 40 da akayi ana zuwa karatu Saudiyya za'a sami Dalibai da dama cikin Kungiyoyin yan ta'adda, amma kuma sabanin hakan ke faruwa, galibin mutanen da ke cikin harkar ta'addanci Jahilai ne, kuma shi Maqari yasan hakan saidai Zalunci da rashin adalci irin nasa ba zasu barshi ya fadi hakan ba, sai ya Jinginawa Saudiyya domin biyan bukatar s
u ta yan Bidi'a.

ALLAH YA YIWA ADDININ SA DAGA SHARRIN MAKIYA SUNNAH, YA TSARE BILADUL HARAMAIN DAGA SHARRIN KAFIRAI DA MUNAFUKAI DA YAN BIDI'A.

Attahiru Muhammad Marnona
Madina, Saudiyya
19-10-2017

Share this


Author: verified_user

0 Comments: