Labarai

Bambancin Akida Ne Ya Sa Aka Maka Sheik Kabiru Gombe A Kotu Saboda Gidansa, Inji Lauyansa

kotu ta yi fatali da karar

A karshe dai kotun shari’ar Musulunci da ke birnin Kano ta sallami karar da makwabcin  fitaccen malaman addinin Islama, Kabiru Gombe ya shigar gabanta bisa tuhumarsa da gina maka-makan tagogi da za su ba shi damar leken gidajen makwabta.

Jaridar Alfijir ta ruwaito hakan ya biyo bayan shaidar da mai karar, Mu’awiyya Aminu Sagagi ya bayar ne a gaban kotun mai lamba 2 cewa  Kabiru Gombe ya sauya fasalin tagogin bayan da maganar ta isa gaban kotu.

Idan dai baku manta ba a kwanakin baya majiyar ta mu ta ruwaito cewa makwafcin Shehin malamin mai suna Mu’awiyya Aminu Sagagi ya shigar da karar Sheikh Kabiru Gombe bisa zargin cewa zai iya leka cikin gidansa ta tagogin gidan da suke makwabtaka a unguwar Sabuwar Gandu, Kano.

Bayanai sunce Alkalin kotun, Ibrahim Sarki Yola ya ce kotun ta gamsu da gyaran da malamin ya yi amma ya umarce shi da ya tabbatar cewa bai kara  bude tagogin a nan gaba ba.

Kodayake dai lauyan Kabiru Gombe, Ishaq Adam Ishaq ya shaidawa manema labarai cewa babu abunda aka cenza a ginin yadda gidan ya ke a yanzu haka yake tun asali, yace kawai sabanin akida ne ya sa aka gurfanar da malamin a gaban kotu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button