Thursday, 5 October 2017
Ayi hattara Sabuwar cuta mai suna “monkeypox” ta ɓarke a jihar Bayelsa

Home Ayi hattara Sabuwar cuta mai suna “monkeypox” ta ɓarke a jihar Bayelsa
Ku Tura A Social Media
Al’ummar jihar Bayelsa na cikin tashin hankali barkewa wata sabuwar cuta makamanciyar cutar kyanda mai suna “monkeypox”.
An killace mutane 11 ciki har da wani likita wanda cutar ya kamu da su a asibitin koyarwa na jami’ar Niger Delta dake garin Okolobiri nan jihar Bayelsa.
Kwamishnan lafiya na jihar farfesa Ebitimitula Etebu ya tabbatar da ɓarkewar inda ya kara da cewa an tura samfurin ƙwayoyin cutar zuwa ga dakin gwaje-gwaje na hukumar lafiya na duniya dake nan Dakar a ƙasar Senegal .


Kwamishnan yace akalla mutum 49 wadanda ake zaton sun kamu da cutar ake nema don a kebe su.

Cutar wanda aka fara gano a kasar DR Congo kana ya barke zuwa ga ƙasashen yankin yammacin Afrika ya samu asali ne daga jikin biri da sauran dabbobi dake shiga daji kamar kurege da bera da barewa.

Etebu yayi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalin su domin an raba na’urorin tsaro ga yan aiki domin kariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: