Friday, 27 October 2017
Ali Nuhu Dalilin da yasa na karfafa gwiwan Rahama sadau wajen bada hakuri

Home Ali Nuhu Dalilin da yasa na karfafa gwiwan Rahama sadau wajen bada hakuri
Ku Tura A Social Media
Jarumin yace Rahama ta yarda da bada hakurin ba tare da an tilasta mata hakazalika tayi hakan bayan ta gane cewa tayi kuskure kuma yayi ikirari cewa shi dan Adam ajizi ne wanda baya rabuwa da yin kuskure


Fitaccen jarumin kuma mai tauraro Ali Nuhu shine kashin bayan kokon bara da jaruma Rahama Sadau tayi na neman gafara bisa ga abun da ya faru a baya wanda yayi sanadiyar korarta daga farfajiyar kannywood.

A rahoton da jaridar Dailytrust ta fitar Ali Nuhu yace jarumar ta bada hakuri bayan ta gane cewa tayi kuskure, yayi ikirari cewa dan Adam ajizi ne wanda baya rabuwa da aikata kuskure.

" A matsayin mu na manya a masana'antar, ya zama dole mu wayar da kan kananan jarumai na dandalin, shiyasa na karfafa mata gwiwa wajen bada hakuri"

"Yana da kyau idan mutum ya gane kurakuran shi ya bada hakuri. Rahama tayi kokari da ta bada hakuri kuma ta dau alkawari cewa baza ta kara aikata kuskuren ba. Ta aika wa kungiyar MOPPAN wasikar neman gafara wanda na san membobin kungiyar suna tattaunawa akai" Inji Ali Nuhu.
Ita dai Rahama Sadau ta fito fili ta baiwa jama'a hakuri bisa ga kuskuren da tayi wanda yasa aka koreta daga dandalin kannywood.
Tayi hakan ne yayin data ziyarci gidan rediyo na
Rahama Fm dake jihar Kano cikin wani shiri mai suna "ku karkade kunnuwan ku".

Share this


Author: verified_user

0 Comments: