Thursday, 19 October 2017
Ali Nuhu Da Ahmed Musa Sarakuna Biyu Sun Kulla Aminchi (kalli Hotuna)

Home Ali Nuhu Da Ahmed Musa Sarakuna Biyu Sun Kulla Aminchi (kalli Hotuna)
Ku Tura A Social Media
Daga Maje El-Hajeej Hotoro, Kano.

Shahararren tauraron shirin fina-finan Hausa Ali Nuhu Mohammed wanda tsawon shekara da shekaru, ya ke rike da kambun sarautar Sarkin Kannywood. Aminci da kyakkyawar alaka ta kullu tsakaninsa da Shahararren dan wasan kwallon kafar Najeriya Ahmed Musa. Wanda shima a halin yanzu ya ke rike da kambun sarautar Sarkin Kwallon kafa na jihar Kano.

Ali Nuhu a kwanakin baya ya yi tattaki takanas ta-kano zuwa kasar Ingila inda ya ziyarci Ahmed Musa da ke buga kwallo a kungiyar ta Leceister City. A yayin wannan ziyara ya kewaya da Ali Nuhu zuwa sassan kungiyar kwallon kafar.

Tun daga nan sai ya zamanto kusan kowane sha'anin Ahmed Musa za ka ga Ali Nuhu a wajen. Kamar nadin sarautar Shugaban Matasan Arewa da kuma yayin bikin daurin auren sa. Kazalika an ga Ali Nuhu a yayin bude sabon gidan wasan kwallo da motsa jiki da Ahmed Musa ya bude a unguwar Hotoro da ke jihar Kano.

Majiyar SARAUNIYA ta jiyo cewa, Ali Nuhu yana da karfin fada aji dangane da sha'anin Ahmed Musa. Sakamakon kyakkyawar alakar da ke tsakanin su. Ko yayin halartar buga wasan Najeriya da Zambiya suna tare a lokuta da dama a jihar Kano.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: