Thursday, 26 October 2017
Aisha Buhari Uwargidan shugaban kasa ta mayar da martani bisa ga zargin da dan majalisa yayi

Home Aisha Buhari Uwargidan shugaban kasa ta mayar da martani bisa ga zargin da dan majalisa yayi
Ku Tura A Social Media
Dan majalisar dattawa yayi zargin cewa sufeton yan sanda ya baiwa uwargidan shugaban kasa motoci biyu don amfanin kanta.

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta musanta zargin da sanata Isa Misau yayi na cewa babban sufeton yan sanda ya bata motoci biyu domin amfanin ita kadai.

Sanata Misau yayi wannan zargin ranar laraba yayin da ya gabatar da kanshi a gaban kwamiti masu binciken zargin da yake yi kan sufeton yan sandan Nijeriya.

Matar shugaban kasa ta mayar masa da martani ranar alhamis a shafin ta na twitter inda ta rubuta
"Har yanzu ina amfani da motoci mallakar kaina".

Tun ba yau ba dan majlisar ke zargin sufeto janar
Ibrahim Idris da aikata abubuwa da suka sabawa tsarin hukumar yan sanda.

Dalilin zargin da yayi gwamnatin tarayya ta maka shi kotu bisa ga zargin cin fuska ga babban sufeton.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: