Wednesday, 11 October 2017
Aikin Tonon Man Fetur Na Gwamnatin Buhari Ya Yi Nisa A Jihar Bauchi

Home Aikin Tonon Man Fetur Na Gwamnatin Buhari Ya Yi Nisa A Jihar Bauchi
Ku Tura A Social Media
Daga Ahmadu Manaja Bauchi
Saura kiris Bauchi ta shiga cikin jihohi masu arzikin man fetur a Nijeriya. Buhari da Maikanti Baru aikin ku na kyau, mun gode.

Yanzu haka aikin hako man fetur da iskar gas, da gwamnatin talakawa karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi a jihar Bauchi ya yi nisa.
An dauki wadannan hotuna ne na a lokacin da gwaman jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya kai ziyarar nuna goyon bayan sa akan wannan aiki da gwamnatin Buhari keyi na tono man fetur a jihar Bauchi.
Gwamnan Bauchi ya nuna jin dadin sa da wannan aiki wanda yanzu haka ake saka ran cewa daga yanzu  jihar Bauchi za ta shiga cikin jihohi masu arzikin man fetur a Nijeriya.
Gwamnan jihar Bauchi ya shaidawa Ma'aikatan da ke gudanar da wanan aiki cewa talakawan jihar Bauchi da ma gwamnatin sa, za su bada hadin kai dari bisa dari domin wannan aiki ya yi nasara.

Mu mutanen jihar Bauchi muna fatan alkairi ga gwamnatin talakawa na Baba Buhari, da shi kansa Shugaban kamfanin man fetur na kasa, NNPC, Dr Maikanti Kacalla Baru.
Fatan mu da kuma addu'ar mu shine Allah ya baku sa'a da nasara a wannan aiki.
Buhari Allah ya kara lafiya da nisan kwana mai albarka.
Mai kanti baru, Allah ya kareka Allah ya dauraka akan makiyanka. Man fetur dai saura kiris a jihar Bauchi.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: