Friday, 22 September 2017
Yan wasan ƙwaikwayo na kannywood sun samu matsayi a shirin ''MTV shuga''

Home Yan wasan ƙwaikwayo na kannywood sun samu matsayi a shirin ''MTV shuga''
Ku Tura A Social Media
Rahama da Yakubu zasu nuna kwarewarsu cikin wannan shirin mai ilimantarwaShirin “shuga” wadda gidan talbijin na MTV ke gabatarwa, shirin ne wanda ke wayar da hankulan mutane akan abubuwan dake faruwa cikin al’umma.
Karo na shidda ta wannan shirin ya samu sabin fuskoki ciki har da fittatu yan wasan kannywood.

Yakubu Muhammed da Rahama Sadau.
Rahama da Yakubu zasu nuna ƙwarewarsu cikin wannan shiri mai faɗakar da mutane.
Wannan sabon shirin zai faɗakar da mutane akan yadda za’a kayyade iya yawan yara, yadda za’a hana cutar kanjamau da ilimantar da mutane a kan ilimin jima’i.

MTV Shuga shiri ne wadda ke bada labarin ƙalubalen da matasa ke fuskanta a cikin al’umma tare da yanda zasu kawar da ita kuma wannan sabon shirin zai gabata cikin Nijeriya .

Share this


Author: verified_user

0 Comments: