Wednesday, 20 September 2017
Tsohon dan ƙwallon Manchester United zai koma wassan dembe 'boxing'

Home Tsohon dan ƙwallon Manchester United zai koma wassan dembe 'boxing'
Ku Tura A Social Media
Dan ƙasar Ingila mai shekaru 39 zai sanar ma duniya cewa ya koma wasan dembe ranar talata

Tsohon mai tsaran bayan ƙungiyar Mancheester United Rio Ferdinand zai yi wani gangarimin sanarwa ranar talata.
Ferdinand wanda ya buga wassani 300 ma Manchester United yace tun ba yau ba yake sha’awar dembe kuma yawan koyi da yake yi a dakin motsa jiki ya silar daukan hukuncin na koma fannin wasan dambe.
Dan ƙasar Ingila mai shekaru 39 zai sanar ma duniya cewa ya koma dembe ranar talata.
Tsohon dan wasan wanda ya rasa matar shi sanadiyar ciwon daji zai nemi ya shawo kan hukumar wasan dembe na Ingila kana ya samu lasisi.
Wannan shine karo na biyu da dan wassan ƙwallon kafa zai koma yin Dembe, tarihi ya nuna cewa shima tsohon dan wasan Sherfield United Curtis Woodhouse ya koma dembe har ma ya samu laƙani a cikin shekara 2012.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: