Friday, 15 September 2017
Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Amurka, Daga Nan Ya Wuce Ingila

Home Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Amurka, Daga Nan Ya Wuce Ingila
Ku Tura A Social Media


Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa New York babban birnin kasar Amurka a ranar Lahadi domin halartar taron kasashen duniya karo na 72.

A sanarwar da Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, ya ce Mista Buhari zai halarci taron walima da sakataren dinkin duniya, Antonio Guterres, ya shirya sannan da tattaunawa kan batutuwa daban-daban na hadin kan kasashe.

Adesina ya kuma tabbatar da cewa, Shugaba Buhari zai kuma yi walimar cin abincin dare da shugaban Amurka, Donald Trump da sauran shugabannin duniya.

Shugaban zai samu rakiyar Gwamnonin jihohin Zamfara, Ebonyi da Ondo da kuma wasu daga cikin manyan ministocinsa.

Haka kuma shugaba Buhari zai biya ta Ingila kafin ya komo gida Nijeriya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: