Monday, 4 September 2017
Shugaba Buhari Ya Ki Ganawa Da Ganduje A Daura

Home Shugaba Buhari Ya Ki Ganawa Da Ganduje A Daura
Ku Tura A Social Media

A ranar Asabar din da ta gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya watsawa gwamnan jihar Kano  Abdullahi Umar Ganduje kasa a ido sakamakon kin ganawa da ya yi  da shi a Daura, kamar yadda majiyarmu ta jaridar DAILY NIGERIAN ta tabbatar.

Ganduje ya yi tattaki takanas ta-Kano ne domin ganawa da Buhari wanda yake hutun mako guda a Daura. Jim kadan bayan bijirewa ganin Ganduje da Buhari ya yi, nan take jami'an tsaro suka nemi tawagar Ganduje su gaggauta barin harabar gidan Shugaba Buhari dake Daura.

Jaridar ta kara da cewa, wannan ya sa Gwamnan cike da takaicin da aka yi masa ya yanke shawarar kai ziyara ga 'yar Buhari, sannan kuma ya tsaya kallon hawan Daushe a nan Daura.

Sotuces:facebook/rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: