Friday, 29 September 2017
Salihu Dasuki:-Ɗan arewa da ya kafa tarihi a jami’ar ƙasar Ingila

Home Salihu Dasuki:-Ɗan arewa da ya kafa tarihi a jami’ar ƙasar Ingila
Ku Tura A Social Media
Salihu Dasuki ya samu digiri na uku daga jami’ar dake kasar Ingila kuma ya zama mataimakin Farfesa a fannin ilimin na’ura mai kwakwalwa a jami’ar Amurka dake Nijeriya watau ABTI dake Yola

Wani dan arewa Salihu Dasuki ya zama abun alfahari a ƙasar mu Nijeriya yayin da ya zama babban malami mafi karancin shekaru a jami’ar Sheffield Hallam dake Britaniya.
Wannan dan Nijeriya mai shekaru 29 ya sanar da babban matsayin da ya samu a shafin sa na twitter ranar litinin 25 ga watan Satumba .

“Godiya ta tabbata ga Allah, ba wai zan koma a matsayin mai karancin shekaru, zan koma a matsayin babban malami mafi karancin shekaru a jami’ar Sheffield Hallam” ya rubuta.
Dasuki ya kasance mai matsayi na farko yayin da samu digiri na farko daga jami’ar Eastern Mediterranean University dake arewacin kasar
Cyprus yana da shekara 21 . Ya samu digiri dinsa na biyu da na uku daga jami’ar Brunnel dakeIngila. Ya zama likitan boko yana da shekara 24.

Tunda yayi wannan sanarwar yan Nijeriya nata jinjina mai tare da yi mai fatan alheri game da matsayin da ya samu. Shima kakakin shugaban ƙasa Mallam Garba Shehu ya yaba ma wannan jarumin inda shima ya kara watsa labarin a shafin sa na twitter.
Hakika yan Nijeriya na taka muhimmiyar rawa a fannin karatu a ƙasashen waje.

Muna ma Dr. Salihu Dasuki fatan alheri.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: