Saturday, 16 September 2017
Rikicin shiyyar Inyamurai: Dakta Isa Ali Pantami yayi muhimmin kira ga yan Arewa

Home Rikicin shiyyar Inyamurai: Dakta Isa Ali Pantami yayi muhimmin kira ga yan Arewa
Ku Tura A Social Media

Yayin da rikicin kabilanci ke ci gaba da wakana a garin Aba dake a jihar Abia can cikin yankin kudu maso gabashin kasar nan na yan kabilar Ibo, shahararren malamin Islaman nan kuma shugaban hukumar gwamnatin tarayya dake kula da fasahohin zamani Dakta Isa Ali Pantami yayi muhimmin kira ga yan arewa.

Dakta Pantami yayi kira ga musulmai yan arewacin Najeriya da ma duk inda suke cewa su tabbatar da cewa rai ko daya bai salwanta ba ta sanadiyyar su a yankunan nasu.

 shahararren malamin ya kuma kara da cewa addinin musulunci kwata-kwata bai yadda da daukar doka a hannu ba yayin da kuma yace ba a taba gyara kuskure da wani kuskuren.

Daga nan ne kuma dai sai malamin yayi kira ga hukumomin da abun ya shafa da su tabbatar da tsaron rayukan yan arewa da musulmai a duk inda suke a fadin kasar tare kuma da tabbatar da bin doka da oda.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: