Saturday, 16 September 2017
Rahama Sadau Zata Ci Gaba Da Shirya Finafinai A Kamfaninta

Home Rahama Sadau Zata Ci Gaba Da Shirya Finafinai A Kamfaninta
Ku Tura A Social Media
Daga Fimhausa

Fitacciyar Jarumar fina-finan Hausa Rahma Sadau, za ta ci gaba da shirya finafinai nata na kanta a kamfanin ta na "Sadau pictures"

Kuma jarumar ta bi hanyoyi iri daban-daban domin tallata fina-finanta a wajen masu kallo.

Wannan matakin ya biyo bayan dagewar da hukumar tance finafinai tayi akan kin tance duk wani fim da aka sa jarumar a ciki, hakan ne ya tilastawa masu shirya finafinai daina sa jarumar a fina-finan dan gudun samun matsala.

Yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa domin fara daukar wani sabon fim na kamfaninta bayan Rariya wanda aka haska a wasu manyan Cinemomin kasar nan baki daya.

Ba wani sabon labari bane cewa Rahama Sadau yanzu tafi fitowa a finafinan kudu na Turanci  wanda ya zuwa yanzu tayi fim da yawa daga ciki akawai, Son of Caliphate season 1&2, The light will come, Ajuwaya, Hakkunde da kuma shirin television na Super Story tare da Sani Danja.

Akwai kuma wani sabon shirinta da zai fito ranar 8 ga September da muke ciki mai suna TATU, wannan fim abin kallo ne domin abubuwan mamakin da suke ciki, fim din ya tara manyan Jaruman Kudu.

Akwanakin baya ne kuma Jarumar taje America don yin wani fim tare da fitaccen mawaki Akon mai suna America king.

Korar jarumar dai daga hausa fim ya zama mata kamar wani Gabarar titi ne a jos. domin a kwanaki baya ma babbar jaruma Priyanka Chopra ta kasar India ta bayyana aniyarta na son haduwa da Rahama Sadau.

A yanzu haka Jarumar ta gama daukar wani sabon shirin kamfanin 2effect na turanci mai suna Fantsatic 4 tare da Yakubu Mouhammad.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: