Saturday, 23 September 2017
Rahama Sadau Jarumar Kannywood zata jagoranci bikin gane fitattun yan wasa na masana'antar Nollywood

Home Rahama Sadau Jarumar Kannywood zata jagoranci bikin gane fitattun yan wasa na masana'antar Nollywood
Ku Tura A Social Media
Raham zata hada gwiwa da Gbenro Ajibade wajen gabatar da bikin gane ƙwararrun yan wasan Nollywood na BanaWannan fitacciyar yar wassan fina-fina- na masana’antar kannywood Rahama Sadau ta samu wani sabon daraja inda zata gabatar da bikin gane fitattu yan wasan masana’antar nollywood.
Rahama zata hada gwiwa da fittacen dan wasan masana’antar Nollywood Gbenro Ajibade wajen gabatar da bikin wadda wakana cikin watan Disemba a Jihar Ogun.
Fitacciyar jaruma ta samu yabo da dama daga wadanda suka shirya bikin BON award inda suka ce jarumar tana da basira kuma ta nuna cewa basirar ta a ko wani masana’anta take iya amfani da ita.

Jarumar ta nuna farin cikin ta game da wannan damar a shafinta na instagram tare da daura hotunan ta tare da abokin aikin ta na bikin.
Wani mai ruwa da tsaki na BON Award Seun Oloketuyi yace jaruman da zasu gabatar da bikin na wannan shekarar kwararru ne kuma suna da basirar gabatar da bikin kuma kowa zai yi farin ciki da haka.

BON Awards bikine wanda ake gudanar ko wani shekara domin gane yan wasan da suka fice ko wani shekara a masana’antar Nollywood.
Ita ma dai Rahama Sadau tana cikin yan takarar yan wasan (mata) da suka fice cikin wannan shekarar sanadiyar fitowar ta a shirin ‘TATU’.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: