Friday, 29 September 2017
Psquare:-Shahararren mawaka yan uwan juna sun gwabza a ofishin alkalin su (Bidiyo)

Home Psquare:-Shahararren mawaka yan uwan juna sun gwabza a ofishin alkalin su (Bidiyo)
Ku Tura A Social Media
Tun ba yau daya daga cikin tagwayen ke yancin zama da kanshi domin baya jin dadin abubuwa dake faruwa tsakanin shi da yan uwanshi
Bidiyo mai nuna yanda shaharraren mawaka Psquare suna gamawa a offishin alkalin su yana ta yawo a yanar gizo.

Cikin bidiyon wanda daga daga cikin tagwayen ya ɗauka, yan uwan suna ta zage-zage har ma zasu soma fada tsakanin su.
Wannan ya fito kwana biyu bayan daya daga cikin tagwayen Peter Okoye ya tura wasika daƙile ga domin yana son a sauke yerjeniyar dake tsakanin shi da yan uwan sa.
Labari na nuna cewa, Peter ya nemi a sauke yerjejeniyar ƙwangilar ƙungiyar domin baya son ya ci amanar matar shi da yaran shi don moriyar ƙungiyar.
Peter ya ruwaito cewa dan uwan shi Paul ya soke wasan da zasu yi a Amurka ba tare da izinin ba tare da wasu wasannin da dama.

Yayi ikirari cewa babban wan su Jude Okoye yayi barazanar kashe shi a gaban dan uwan shi Paul da matar tsohon gwamnan jihar Cross rivers Mrs Imoke.
Shi dai Peter yace ji ma iyalin shi tsoro domin barazanar da yan uwan shi keyi gare su.
Wannan ba shi bane karo na farko da yan uwan zasu nuna rashin datuwa tsakanin su ga bainar jama’a.
Wannan ƙiyayyar ya faru bayan wasu maganganun da yan uwan suka yi ma junan su a shafukar su ta yanar gizo.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: