Monday, 18 September 2017
Nigeria: Malaman Jami'o'i sun janye yajin aiki

Home Nigeria: Malaman Jami'o'i sun janye yajin aiki
Ku Tura A Social Media
Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta shiga na sai-baba-ta-gani bayan sama da wata daya.
Shugaban kungiyar farfesa Biodun Ogunyemi ne ya sanar da janyewar, ranar Litinin da daddare jim kadan bayan wata ganawa da Ministan kwadago da ayyuka, Dakta Chris Ngige, a Abuja.
Kungiyar ta ce ta dakatar da yajin aikin ne wanda ta shafe wata daya da kwana shida, har zuiwa karshen watan Oktoba, lokacin da gwamnati za ta cika alkawarun da ta yi.
Matakin dai ya biyo bayan tarukan tattaunawar da aka rika yi ne tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, musamman ma'aikatar ilimin da kuma ta kwadago da ayyuka.
Kungiyar ta umarci malaman jami'o'i da su koma bakin aiki daga ranar Talata.
Kungiyar ta ASUU ta shiga yajin aikin ne na sai-abin-da-hali-ya-yi, ranar 13 ga watan Agusta, sakamakon gazawar gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi a watan Nuwamba na 2016.

Rahoto daga:bbchausa.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: