Monday, 18 September 2017
Mabiyan tsohon shugaban jam’iyar PDP guda 14,00 sunyi balaguro zuwa jam’iyar APC

Home Mabiyan tsohon shugaban jam’iyar PDP guda 14,00 sunyi balaguro zuwa jam’iyar APC
Ku Tura A Social Media
Sama da mutune 14,00 na jam’iyar PDP kuma mabiyan tsohon shugaban jam’iyar Ali Modu Sheriff suka yi balaguro zuwa jam’iyar adawa na APC.
An samu labari cewa tsohon mataimaki shugaban jam’iyar PDP Dr. Cairo Ojuogbo ya jagoranci masu balaguron zuwa jam’iya mai ci.
Ojuogbo yace sun gaji da rtashin hukunta masu laifi da jam’iyar keyi wadda yayi sanadiyar rashin nasara a zaben 2015 shiyasa suka bar jam’iyar.
Mabiyan sun samu karbuwa a APC na karamar hukumar Agboh dake jihar Delta.
Cikin manyan baki da suka tarbi su akwai mataimakin shugaban jam’iya na ƙasa Mr Hilliard Eta , wani jigon jam’iya na jihar Delta Olorogun O’otega Emerhor , ministan man fetur Ibe Kachukwu da shugaban jam’iya na jihar Prophet Jones Erue .
Ojuogbo ya kara da cewa tawagar Ahmed Makarfi bata amince dasu tunda kotu ta kori tsohon shugaban jam’iyar Ali modu Sheriff.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: