Saturday, 30 September 2017
Lil-Ameer Mahaifiyar marigayi tana mamasoyan shi godiya game daaddu’o’in da suke yi

Home Lil-Ameer Mahaifiyar marigayi tana mamasoyan shi godiya game daaddu’o’in da suke yi
Ku Tura A Social Media
Hajiya Maimuna Hassantace bata taba sanin cewa ɗanta
yana da masoya sosai sai da alamarin ya faru

Mahaifiyar marigayi Ameer Hassan wanda aka sani da lil-
ameer ta ma masoyan shi godiya game da addu’o’i tare da
fatan alheri da suke yi ma iyalin shi.
A wata hira ta musamman da tayi da Arewa24 Hajiya
Maimuna Hassan tace bata taba sanin cewa danta ya kai
matsayin da ya kai sai da ajalin shi ya taho.
“Masoyan Ameer ina maku godiya da goyon baya da kuka
bamu, da wanda suke Nijeriya har da kasashen waje muna
ganin sakonin ku, mun gode kuma Allah ya saka maku da
alheri.
Bamu taba sanin Ameer yana da masoya sai da abun ya faru,
mun gode muna muku godiya” tace.
Mahaifiyar tace tana kewar marigayi tare da yaba halayyar shi
na yaron kirki ne kuma mai nagartaccen halin ne kuma yana
so mahahafiyar shi sosai.
Tayi kira ga sauran iyaye da su mara ma yaran su baya indai
suna da burin yin waka ba wai su tilasta masu wani buri
daban.
Marigayi ya rasu sanadiyar hatsarin da ya samu saman babur
hanyar shi zuwa gida a garin Kano.
Allah ya jikan shi da rahama... Ameen.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: