Saturday, 16 September 2017
Kanwar Samira Ahmad Ta Fara Fim Da ƙafar Dama

Home Kanwar Samira Ahmad Ta Fara Fim Da ƙafar Dama
Ku Tura A Social Media
Abdul Amart Maikwashewa ya shirya Gabatar da sabuwar Jaruma acikin fim dinsa mai suna Ranar Aurena, Aseeya Ahmad kanwace ga tsohuwar Jaruma Samira Ahmad wadda itama ta taka mihimmiyar rawa a duniyar kannywood kafin aurenta da angonta TY sha'aban.

Aseeya kyakkyawace sannan masu sharhi akan jaruman kannywood suna Hasashen cewa jarumar zata fara da kafar dama domin Ganin ta bulla a kamfanin "Abnur Entertainment" sun dade suna Gabatar da manyan finafinai, Irinsu Aisha Humairah, Ummi, Ma'aurata, Zeenat, Mijin Biza da kuma Minal, wadannan wasu da cikin manyan finafinai ne wadanda kamfanin suka gabatar.

Abnur ( Ab-dulNur-a) bisa hadin Gwiwar abokan juna Nura M Inuwa da Abdul Amart sun fara daukar fim din a ranar Laraba 16 ga Augusta, wanda zai samu aiki daga Babban Darekta Sadiq N Mafia.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: