Tuesday, 19 September 2017
Kannywood:- Shahararren Jarumin nan Ali Nuhu: Abinda yasa baza mu saki fim din Mansoor Ba

Home Kannywood:- Shahararren Jarumin nan Ali Nuhu: Abinda yasa baza mu saki fim din Mansoor Ba
Ku Tura A Social Media
Fitaccen Jarumin Kannywood Ali Nuhu ya bayyana dalilin da ya sa ba za a fara sayar da faya-fayen sabon fim din Masoor ba.
A zantawarshi da Ibrahim Isa, Ali Nuhu ya ce za a ci gaba da nuna fim din a sinima ne har sai mai fim din ya samu yadda yake so domin gudun masu satan fasaha su far ma fim din.
Fim ɗin Mansur, wanda fitaccen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya shirya kuma ya ba da umarni, labari ne na wani matashi ɗan gaba da fatiha.
Mahaifiyar Mansur ta yi ƙoƙarin ɓoye masa wannan sirri game da asalinsa, sai dai soyayya ta sanya shi neman sanin gaskiyar al’amari.
Iyayen wata yarinyar da soyayya ta hada su a sakandare ne suka yi masa gorin asali, inda hakan ya tilasta masa katse karatu, ya bazama duniya don gano mahaifinsa.
An ƙaddamar da fim ɗin Mansoor ranar Alhamis ta hanyar nunin farko, a wani gawurtaccen biki cikin wata silima da ke birnin Kano, kuma sai a nan gaba ne za a fitar da faya-fayensa na bidiyo.
Sama da shekara goma da fara tunanin wannan fim, wanda aka shafe fiye da shekara biyu ana tsarawa da haɗa shi.
Daraktan fim ɗin, Ali Nuhu ya ce jigon Mansoor shi ne juriya da tawakkali don samun waraka ga wani halin alhini da ɗan’adam ka iya fuskanta a rayuwa.
“Akwai soyayya a cikinsa, amma jigonsa ba soyayya ba ce. Darasin da yake ƙoƙarin isar wa al’umma shi ne duk abin da ka ga ya samu mutum a rayuwa…kar ka yi masa gori.
Kar ka tsangwame shi a kan wannan abu. Domin mai yiwuwa hanyar da Allah ya jarabce shi kenan, kamar yadda kai ma a matsayinka na ɗan’adam akwai hanyar da Allah ya jarabce ka.”
Saɓanin yadda aka saba ganin fitattun jarumai a fina-finan Kannywood, a wannan karon an yi amfani da wasu sabbin fuskoki a matsayin manyan jarumai, da suka haɗar da Umar M Sharif da Maryam Yahaya.
Sama da shekara 20 kenan da fara harkar fina-finan Kannywood, amma masu sharhi na sukar cewa ba a sanya fasahar zamani sosai a cikin fina-fianan.
Sai dai masu fim ɗin Mansoor sun ce sun yi ƙoƙarin tunkarar wannan ƙalubale wajen haɗa shi, don haka ne ma a cewarsu, fim ɗin ya kasance mafi tsada a duniyar Kannywood, don kuwa an kashe kusan naira miliyan takwas wajen hadawa da tallata shi.
Source: BBC Hausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: