Saturday, 30 September 2017
kannywood:-Farawa da iyawaJaruman “mansoor” zasu karahaskawa cikin wani sabon fim

Home kannywood:-Farawa da iyawaJaruman “mansoor” zasu karahaskawa cikin wani sabon fim
Ku Tura A Social Media
Sabon tauraruwar Kannywood Maryam Yahaya zata kara
fitowa cikin wani sabon fim tare da shahararren mawaki Umar
M.Sherrif.
Bayan fitowar su cikin shirin wanda tayi tasiri, zasu kara
haskawa cikin wanan sabon fim wanda kamfanin Maishadda
zata dauki nauyin kawowa.
Bisa ga yanda mai shirya fin a-finan hausa Abba Maishadda
ya sanar jaruaman zasu fito cikin sabon shirin fim mai suna
“M.A.R.I.Y.A”.
Sabon shirin Abba Maishadda zai shirya ta kana Ali Nuhu zai
bada umarni.
A hirar da tayi a baya Maryam ta bayyana cewa tun fitowar ta
a cikin shirin 'Mansoor' tauraron ta ke haskawa.
Jarumar ta sanar cewa zata koma makaranta tare yin fim
domin yin fim ba shi kadai bane a gaban ta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: