Tuesday, 19 September 2017
Jarumi Ne Kadai Zai Iya Abinda Shugaba Buhari Ya Yi A Yau

Home Jarumi Ne Kadai Zai Iya Abinda Shugaba Buhari Ya Yi A Yau
Ku Tura A Social Media
Daga M Inuwa M.H

Hakika wannan magana ta shugaban kasa Muhammad Buhari ta birge ni, kuma wannan magana ta saka ni farin ciki da annashuwa a daidai lokacin da na ji shugaba Buhari na caccakar kasar Myanmar akan kashe musilmin Burma.

Sai da na ji kamar na hadiye shi don murna. Wannan shine shugabanci nagari ka fito a taron duniya ka fadi ra'ayinka ba tare da tsoro ba. Wannan jarumta ce.

Allah ya saka maka da alkairi, ysa ka gama mulkin ka lafiya, ya kara maka lafiya.
Shugaba mai karfin hali ba shi da cikakkiyar lafiya, amma ya sadaukar da kansa ga al'umma. Wannan shine shugaba abin tunawa a tarihin Nijeriya.

Muna maka kyakkyawan zaton samun nasarar cikawa Nijeriya alkawarin da ka dauka Baba Buhari.

MH ISMOG

Share this


Author: verified_user

0 Comments: