Sports

FIFA ta fitar da sabon tsarin jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce zata yi amfani da sabon rahoton da zata wallafa a ranar 16 ga watan Oktoba, na kasashen da suka fi kwarewa a fagen kwallon, wajen tsara jadawalin yadda kasashe da zasu fafata da juna a matakin rukuni na Gasar Cin Kofin Duniya, wadda za’a fitar da jadawalinta a ranar 2 ga watan Disamba.
A cewar hukumar daga yanzu zata rika tsara jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya ta hanyar duba kwarewar kasashe, a maimakon tsara jadawalin bisa nahiya-nahiya.
Karkashin sabon tsarin na yanzu, FIFA ta ce za’a kasa baki dayan kasashe 32 da zasu fafata zuwa kashi 4, kasashe da suka fi kwarewa guda takwas a kashi guda, sai kuma wadanda ke biye dasu a matakin kwarewar, su ma guda takwas a tukunya daya.
Daga kowane kashi kuma za’a rika dauko guda ana hada ta da sauran kasashen da suke a mataki daban daban wajen shahara.
FIFA ta ce makasudin haka shi ne tabbatar da cewa kowane rukunin Gasar Cin Kofin Duniyar ya samu adalci wajen hada kwararru da wadanda ke biye da su.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button