Monday, 18 September 2017
Dembele zai shafe watanni 4 yana jiyya

Home Dembele zai shafe watanni 4 yana jiyya
Ku Tura A Social Media
Sabon dan wasan gaba na Barcelona Ousmane Dembele zai shafe watanni hudu cif yana jiyya sakamakon raunin da ya samu a cinyarsa, yayin wasan da suka buga da Getafe, inda yayi mintuna 29 kawai.
Hakan na nufin ko a matakin kasa ma, Dembele ba zai samu haskawa kasarsa Faransa ba, a wasannin neman cancantar da zata fafata da kasashen Bulgaria da Belarus a watan Oktoba mai zuwa.
A cikin wannan makon za’a garzaya da Dembele kasar Finland, inda za’a yi masa tiyata.
A ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata ne Kungiyar Barcelona ta cimma matsaya da takwararta ta Borussia Dortmund na sayan Ousmane Dembele kan kudi fam miliyan 97.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: