Kannywood

Dandalin Kannywood: An so in fito a yar madigo a wani fim din kudu amma naki amincewa – Rahma Sadau

Korarriyar shahararriyar jarumar fina-finan nan na Kannywood a da yanzu kuma hadda fina-finan kudu Rahma Sadau ta bayyana cewa an so ta fito a wani fim din ta na fina-finan kudu a matsayin yar madigo amma sai ta ki yadda saboda la’akari da daga inda ta fito watau arewa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da jaridar The Guardian a karshen makon jiya inda kuma ta bayyana cewa tayi haka ne kawai bisa la’akari da daga inda ta taso da kuma martaba al’ada da addinin yankin arewa.
Dandalin Kannywood: An so in fito a yar madigo a wani fim din kudu amma naki amincewa - Rahma Sadau
Dandalin Mujallarmu kuma dai ta samu cewa da take tsokaci game da korar ta da kungiyar fina-finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damammaki na gudanar da sana’arta a dukkan fadin duniya.
Haka nan kuma jarumar ta bayyana rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi sanadiyyar korar tata a matsayin bangaren aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba game da hakan.
Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron Allah a zuciya yake don haka ba dai dai bane ba a rika yi mata kallon ‘yar iska don kawai tana sana’ar ta.

Sources:Mujallarmu.com
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

  1. wama ya sani ko kina yi, dan komae akace kin aikata zan iya yarda.. ta yanda naga mu"amalarki a duniya. nidai burina ALLAH ya shiryeki kafin ki mutu

  2. Shedaniya kije ki fada ma wasu daban don ba tsoron allah kike ba dakina soron Allah da kinyi aure koma ai wannan ba sana'a bane kina tallata kanki ne kawai allah ya shiryeki in ke me shiryiwa ne in kuma ke bamai shiryuwaba ne allah yamana maganinki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button