Friday, 15 September 2017
Ba Za Mu Janye Dakarunmu Daga Abia Ba - Rundunar Soja

Home Ba Za Mu Janye Dakarunmu Daga Abia Ba - Rundunar Soja
Ku Tura A Social Media

Rundunar Sojan Nijeriya ta tabbatar da cewa ba za ta janye dakarunta daga jihar Abia ba har sai ta kammala atisayen da ta yi wa lakabi da " Operation Python Dance" wato shirin rawar kumurci" wanda ta fara a jihohin Kudu maso Gabas.

A jiya ne dai, Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu ya bayar da sanarwar cewa rundunar Sojan Nijeriya ta amince ta kwashe dakarunta daga jihar amma kuma daga baya Kakakin rundunar Sojan, Sani Usman ya musanta ikirarin Gwamnan.

Kakakin rundunar ya nuna cewa an yi wa jawabin Gwamnan gurguwar fahinta inda ya yi karin haske cewa Gwamnan na nufin cewa za a rika rage yawan dakarun ne daga titinan jihar. Ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da shirin nata kamar yadda ta tsara.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: