Saturday, 16 September 2017
An Bayyana Jaruman Da Za Su Jagoranci Sabon Fim Din Abota

Home An Bayyana Jaruman Da Za Su Jagoranci Sabon Fim Din Abota
Ku Tura A Social Media

Ali Nuhu ya bayyana jaruman da zasu jagoranci sabon fim dinshi mai suna ABOTA da zai fara dauka nanda lokaci kadan, Fim ne zai maida hankali akan wasu abokai guda uku daya Dan film, daya Mawaki, daya Dan kwallo.

Ali Nuhu shine shugaban kamfanin FKD wanda zasu shirya fim din yakara da cewa shi zai fito amatsayin Dan fim wanda bai yadda akwai abota ta gaskiya ba, Adam A Zango a matsayin Mawaki wanda zai iya sadaukar da komai saboda abota sannan sai Sadik Sani Sadik a matsayin Dankwallo wanda yake Neman Abota ta gaskiya ido rufe, akwai Jaruma Nafisa Abdullahi wadda itama zata taka rawa sosai, sai Bakuwar fuska duk da dai ba wannan ne karon farko da zata fara fim ba wato Bilkisu Abdullahi.

Ali Nuhu yace Bayan fim din Mansoor wanda aka haska a cinemomi a fadin kasar nan kuma mutane sun yaba aikin sosai yayi alkawarin cewa ABOTA shine zai zama akalar chanji a kannywood.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: