Tuesday, 19 September 2017
Ali Nuhu ya fadi lokacin da fim din mansoor zai fito

Home Ali Nuhu ya fadi lokacin da fim din mansoor zai fito
Ku Tura A Social Media

Ali Nuhu CEO na Kamfanin FKD wadanda suka shirya ya bayyana lokacin da zai saki fim dinsa MANSOOR, Ya bayyana haka ne a shafinsa na twitter inda wani mai yi masa fatan alkhairi ya tamabayeshi cewa " Allah yataimaki Sarki yaushe ne za'a saki fim din Mansoor ? " inda shi kuma ya bashi amsa da cewa karshen watan nan Insha Allah. Tun a farko dai Ali Nuhu ya fadi Dalilaan da yasa bazai saki fim din mansoor ba amma yanzu hakan yana nuna zuwa karshen wannan wata zamu sa ran samun fim din Masoor a kasuwanni da kuma shagunan sai da DVD,
Mansoor labarin wani matashi wanda soyayya tasa ya gano asalinshi, ya hada yanwasa sabbin Irinsu Umar M Shareef, maryam Yahaya da kuma Ali Nuhu, Babale Hayatu,Abba El-mustapha, teema makamashi, baba karami da dai sauransu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: