Monday, 18 September 2017
ABUN MAMAKI :- Ashe Bahaushe Bai Taba Yin Shugabncin Nijeriya Ba?

Home ABUN MAMAKI :- Ashe Bahaushe Bai Taba Yin Shugabncin Nijeriya Ba?
Ku Tura A Social Media


Daga Rabi'u Biyora

Idan muka kalli yawan al'ummar Hausawan dake Nijeriya, da kuma irin cigaban da suka jawowa kasar, amma a ce har yanzu ko sau daya ba su taba samun damar shugabanci a Nijeriya ba...

Ku kalli jerin sunayen 'yan Arewan da suka mulki Nijeriya, cikinsu babu Bahaushe ko guda daya.

1... Tafawa Balewa ...... ?  Ba BAHAUSHE bane

2... Yakubu Gawon .... Kabilar Angas

3.... Murtala Muhammad..... daga Auchi

4..... Shehu Shagari..... Basakkwace

5.... Muhammadu Buhari.... Bafulatani

6..... Ibrahim Badamasi Babangida .... Banufe

7..... Sani Abacha..... Kanuri

8...... Abdulsalam Abubakar ..... Gwari

9..... Musa Yar,adua ...... Bafulatani.....

Wannan dalilin ya sa za mu fara gudanar da kamfen din ganin Bahaushe cikakke shi ma ya samu damar yin shugabancin Nijeriya, nan gaba bayan Buhari ya sauka a 2023.

#Bahausheforpresident2023

Share this


Author: verified_user

0 Comments: