Friday, 15 September 2017
Abubuwa 5 da baku sani ba game da matashi mawakin hausa hip hop

Home Abubuwa 5 da baku sani ba game da matashi mawakin hausa hip hop
Ku Tura A Social MediaHakika masana'antar nishatarwa ta Arewa tayi babban rashi da rasuwar dan matashi mawakin hausa hip hop, amma indai ajalin mutum ya kai babu wanda zai iya kubutar dashi.

Ameer Isa Hassan ya rasu ranar 14 ga watan Satumba a garin Kano sanadiyar hatsarin mota. Anyi jana'izar shi ranar juma'a a layin massalacin juma'a na tarauni.
ga wandada basu san labarin wannan matashin ga abubuwa 5 da ya kamata ku sani;

1. Haifafan Dan jihar kano ne
An haifi marigayi Ameer a cikin 2003 a jihar Kano.

2. Har zuwa lokacin rasuwar sa mawakin yana koyan darasi a makaranta
Duk da kasancewar shi wanda ya fara shahara a harkar wakoki marigayi bai bari harkar ta dauki hankalin shi wajen koyan darasi. ya kan tafi makarantar boko kuma idan ya tashi yaje na islamiyya. sai karshen mako yake samun damar yin aikin waka. babban burin marigayi shine in ya gama karatu ya zama matukin jirgin sama.

3. Iyayen sa sun mara mai baya
hakika iyayen suka bashi damar fara waka kuma uwar take taimaka masa wajen rubuta wakokin.
Ameer ya canza makarantu domin masoyan sa sukan tunkare shi idan yana koyan darasi.

4. Ya fara waka tun yana jjs 1 na makarantar sekandare
matashin ya fara waka ne domin tun yana dan karami yake muradin waka. ya fara waka ne domin ya nuna ma duniya cewa matasa daga yankin arewaci kasar nan na iya rera waka kuma su yi nasara.

5. Yayi wakoki da dama kuma yayi wasa tare da sauran shaharren mawaka.

cikin wakokin da marigayi yayi akwai "boss", "champion", "ilimin boko da addinin musulunci", "dance for me" da dai sauran su.
Matashin wadda ake wa lakabi "karaminsu babbansu" yayi waka tare da shaharraru da dama kuma yayi wassanni da dama a wurare daban-daban#
Allah ya jikanshi da rahama, Ameen.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: