Thursday, 24 August 2017




Kalli Dandazon magoya bayan shugaban ƙasa Buhari Har Yanzu Muna Tare Da Shugaba Buhari, Cewar Kanawa

Home Kalli Dandazon magoya bayan shugaban ƙasa Buhari Har Yanzu Muna Tare Da Shugaba Buhari, Cewar Kanawa
Ku Tura A Social Media



Dandazon magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis sun gudanar da addu'o'i na musamman ga shugaban kasan a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata cikin birnin Kano don nuna farin cikin su da dawowarsa daga jinya da kuma fatan Allah ya kara masa lafiya.

Daga bisani dandanzon jama'an karkashin jagorancin hadimin shugaba Buhari kan kafafun sadarwa, wato Sha'aban Sharada sun dunguma zuwa fadar gwamnatin Kano, inda gwamna Ganduje ya tarbe su.

Gwamnan ya nuna farin cikinsa game da yadda ya ga dandanzon magoyan bayan shugaban kasan, wanda a cewarsa hakan ya nuna cewa har yanzu al'ummar jihar Kano na tare da shugaba Buhari dari bisa dari 

Kalli hotunan dandazon magoya bayan shugaba muhammad buhari














Ku kasance da www.hausaloaded.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: