Wednesday, 2 August 2017
Bamu Da Masaniyar Dawowar Shugaban Kasa A Yau, Cewar Masu Magana Da Yawun Shugaban Kasa.

Home Bamu Da Masaniyar Dawowar Shugaban Kasa A Yau, Cewar Masu Magana Da Yawun Shugaban Kasa.
Ku Tura A Social Media


Biyo bayan wasu rahotanni da suka mamaye kafafen sadarwar zamani a daren jiya, kan batun dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren jiya ko safiyar yau Laraba, sashin watsa labarai na fadar shugaban kasa sun ce basu da masaniya kan wannan batu.

Batun dawowar shugaban kasar dai ya zafafa ne bayan rahotannin da aka samu na cewar jirgin dake jiran shugaban kasa wacce kwanaki baya aka dauko hoton ta a filin fakin na filin saman birnin London ta tashi zuwa Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya ce shi bashi da masaniya akan wannan rahoto. Haka zalika shima Femi Adesina ya ce idan har shugaban kasa zai dawo ana sanar dasu, amma izuwa yanzu basu da wani rahoto dangane da batun.

Yanzu dai ta tabbata cewar babu wani ingantaccen bayani kan dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari gida a yau Laraba

Share this


Author: verified_user

0 Comments: