Thursday, 27 July 2017




Yadda Bezos ya doke Bill Gates a matsayin mai kudin Duniya !!!

Home Yadda Bezos ya doke Bill Gates a matsayin mai kudin Duniya !!!
Ku Tura A Social Media


Kowa ya san cewa Attajiri Bill Gates shi ya fi kowa kudi a Duniya na dogon lokaci tun ba yau. Kwatsam sai ga wani hamshakin mai kudi ya sha gaban shi.

Tun shekaru 24 da suka wuce kenan kowace shekara Bill Gates yana cikin manyan Attajiran Duniya. Mista Bill Gates shi yake da fitaccen Kamfanin nan na Microsoft. 

Bezos ne wanda ya mallaki Kamfanin Amazon da ake saida kayan litattafai da sauran su. Ko bana dai Gates ya kashe Dala Biliyan 3.1 wajen wannan harkar kiwon lafiya a Duniya.

Ba don irin wannan kokari ba dai babu yadda za ayi Bezos ya doke Bill Gates. Ko Bill Gates din zai dawo matsayin sa kamar yadda ya faru a baya? 


Sources :naijhausa.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: