Monday, 3 July 2017
Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un : Allah ya yi wa Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule rasuwa a safiyar Litinin Yau

Home Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un : Allah ya yi wa Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule rasuwa a safiyar Litinin Yau
Ku Tura A Social Media
Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un

Allah ya yi wa Dan masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule rasuwa a safiyar Litinin din nan da safe bayan ya sha fama da jinya.

Maitama sule Ya rasu ne a kasar Masar inda ya yi jinyar rashin lafiyar da ya yi fama da ita.

Marigayi Maitama Sule shaharraren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya rike mukamin minista da kuma jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya.

Dan masanin Kano ya mutu yana da shekara 87 a duniya.

Allah ya jikansa tare da sauran musulmai muminai.

Bilya Yariman Barebarin Fcbk. 
3rd July, 2017.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: