Uncategorized

Hotunan manyan masallatai 10 ma fi kyau a duniya !-bbchausa

Masallacin wani wuri ne na bauta ga mabiya addinin Islama, inda al’ummar Musulmi ke taruwa su yi sallah cikin jam’i.

Akwai gine-ginen masallatai masu kayatarwa a duniya wadanda wata kila ba ku taba sanin da su ba, don haka muka kawo muku wasu daga cikinsu.
1. Masallacin Haramin Makkah da ke Saudiyya

Masallacin Al Haram Mosque - Makkah, Saudi ArabiaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin Al Haram a yanzu ya mamaye kimanin murabba’in mita 400,800, wanda ke daukar mutane miliyan hudu a ciki da wajensa lokacin Hajji.

Al-Qur’ani ya bayyana wannan masallacin a matsayin na farko da aka gina a ban kasa domin dan Adam ya bauta wa Allah.
Wannan masallacin, mai suna Al Haram, wato “Mafificin Masallaci” shi ne ya fi ko wanne daraja a duniya baki daya, yana da dadadden tarihi, ya fi ko wanne masallaci daraja da girma da kayatuwa.
A zagaye yake d a gine-ginen manyan otal-otal masu kyau da tsari wadanda idan kana daga cikisu ma kana iya hango harabar masallacin da cikinsa.
2. Masallacin Annabi SAW da ke Madinah a kasar Saudiyya

Al-Masjid an-Nabawi - Medina, Saudi ArabiaHakkin mallakar hotoKINGDOM OF SAUDI ARABIA MINISTRY OF INFORMATION
Image captionMafi darajar wuri a wannan Masallaci shi ne daga tsakiyarsa, inda kabarin Annabi Muhammad SAW ya ke

Wannan masallacin da aka fi sani da masjid An Nabawi, watau “Masallacin Annabi,” shi ne masallaci na biyu mafi daraja da kyau da girma bayan na Makkah.
Annabi SAW da kansa ya gina masallacin a lokacin da ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina shekara 1439 da ta gabata.
A ciki kabarin fiyayyen halitta yake da na manyan abokansa biyu kuma sahabbansa Abubakar da Umar Allah ya kara musu yarda.
Gidan Annabi SAW a yanzu haka duk ya shiga cikin masallacin.
Ana yi wa masallacin lakabi da ‘Koriyar Hubba ta Dan Abdullahi.’
3. Masallacin Kudus da ke Jerusalem a Isra’ila

Al Aqsa Mosque - Jerusalem, PalestineHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionTarihi ya nuna cewa a baya, Annabi Muhammad SAW na jagorantar sallah ne a yayin da ake fuskantar wannan masallaci, kafin daga wata na 17 na hijira, Allah ya umurce shi da maya da alkiblar zuwa Ka’aba, da ke Makkah

Masallaci na uku mafi girma da daraja a ban kasa.
Ana kiransa da Al-Aqsa kamar yadda ya zo a Al-Kur’ani mai tsarki ko kuma Baytul-Muqaddas.
An gina Masallacin Al-Aqsa ne a garin birnin Kudus da ke kasar Isra’ila.
Masallacin shi kan sa an gina shi ne a wani yanki na Al-Haram ash-Sharif, wato “Mafificin mafaka mai tsarki”, wanda su Yahudawa suke kira Temple Mount, wanda shi ne mafi tsarki su kuma a wurinsu.
Ta Baitul Mukaddas ne Annabi SAW ya tafi Mi’iraji.
4. Masallacin Hassan na Moroko

Hassan II Mosque - MoroccoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin na kallon tekun Atlantika, inda aka shimfida kasa sa da gilashi, ta yadda ake iya ganin cikin ruwa

Wannan masallacin yana birnin Casablanca ne a Moroko, kuma shi ne masallaci mafi girma a kasar, haka kuma na bakwai a jerin masallatai masu girma a duniya.
Hasumiyarsa ita ce wadda ta fi tsayi da kimanin mita 210.
An kammala ginin masallacin ne a shekarar 1993.
Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddin a Brunei

Sultan Omar Ali Saifuddin Mosque - BruneiHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAn zagaye Masallacin da bishiyoyi da furanni da dama, domin kamanta ni’imar Aljannah Firdausi

Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddien, wani masallacin ‘yan sarauta ne da ke garin Bandar Seri Begawan, babban birnin masarautar Brunei.
Ana yi wa masallacin kallon wanda ya fi ban sha’awa a yankin Asiya, kuma wata matattara ce ta masu yawon bude ido a Brunei.
An kammala gininsa a shekarar 1958, kuma yana daya daga cikin gine-gine da ke nuna bajintar taswirar gine-gine a duniya.
6. Masallacin Zahir da ke Kedah a Malaysia

Zahir Mosque - Kedah, MalaysiaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionDuk shekara ake gudanar da musabaka a cikin wannan Masallaci

Masallacin Zahir, shi ne masallacin jihar Kedah, wanda ke kasar Malaysia, wanda ke tsakiyar garin Alor Star.
An gina masallacin a shekarar 1912, da tallafin Tunku Mahmud, dan Sultan Tajuddin Mukarram Shah.
Wannan masallaci babba ne sosai kuma yana da kayan kawa na zamani.
7. Masallacin Faisal da ke Islamabad a Pakistan

Faisal Mosque Islamabad - PakistanHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin Faisal da ke birnin Islamabad a Pakistan shi ne mafi girma a kudancin Asiya, kuma shi ne na hudu da ya fi girma a duniya

Wannan masallacin shi ne mafi girma a kudu maso gabashi da kudancin Asiya, kazalika shi ne na hudu cikin mafi girman masallatai a duniya.
A shekarun 1986 zuwa 1993 shi ne masallacin da ya fi ko wanne girma a duniya, kafin masallacin Hassan na biyu da ke Casablanca a Morocco, da kuma bunkasa Masjid Al-Haram na Makkah da aka yi daga baya, wadanda duk suka doke shi.
8. Masallacin Taj ul da ke Bhopal a Indiya

Taj ul Mosque - Bhopal, IndiaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin na da babban lambu a tsakiyarsa, inda aka dasa wani babban tankin ruwa

Ma’anar sunan wannan masallaci, “Sarkin duk masallatai”, kuma yana garin Bhopal ne a Indiya. Ana gudanar da karatun Qur’ani ma a masallacin, da rana. Masallacin shi ne mafi girma a nahiyar Asiya baki daya.
9. Masallacin Badshahi a Lahore, Pakistan

Badshahi Mosque of Lahore - PakistanHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin na daukar masu ibadah dubu 55 lokaci guda wajen sallah, kuma daga waje yana iya daukar masallata dubu 95

Sarkin daular Mughal, Aurangzeb ne ya kaddamar da Masallacin Badshahi, ko kuma “Masallacin sarauta” da ke Lahore, a shekarar 1673, wanda shi ne masallaci mafi girma na biyu a Pakistan da kudancin Asiya.
Haka kuma shi ne masallaci na biyar mafi girma a duniya. Masallacin ya yi fice a kyau, wanda ya fito da irin kasaitar daular ta Mughal.
10. Masallacin Sultan na Singapore

Sultan Mosque, SingaporeHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAn mayar da wannan Masallacin wani gini na tarihin Singapore a hukumance daga ranar 14 ga watan Maris din 1975

Ana yi wa wannan masallacin da ke layin Muscat da ke gundumar Glam Rochor a Singapore, kallon mafi daraja tsakanin dukkan masallatan kasar. asallacin Sultan ya dade ba tare da an sauya masa komai ba tun da aka gina shi, sai wasu ‘yan gyare-gyare da aka yi a harabarsa a shekarar 1960, da wasu kare-kare da aka yi a shekarar 1993.
©bbchausa.com
Mun Dauko Daga Shafi
n Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button