Kannywood

Banbancin Aminu Alan (waka) Da Sauran Mawakan Zamani !!!

Ban cika son yin magana akan Aminu Alanwaka ba, saboda ina jin Kamar ina magana ne a kaina.
Ba ni daga cikin mutanen da su ke da ra’ayin Ala yafi kowa iya waka ko dadin murya. Abinda na sa ni game da Ala kuma zan iya fadi ko a gaban Sarki shine,Alanwaka na da hangen nesa a duk al’amura.

Duk wakar da Ala zaiyi sai yayi dogon Nazari da bincike gami da hangen yadda al’ummah za su kalleta. Ga duk Wanda ke bibiyar Alanwaka a wakokinsa na siyasa zai amince da ni. A wakokin Siyasar da yayi a baya idan za mu saurare su, za mu ga bai zage damtse domin zagin wasu ko cin mutuncin wasu ba. Misali idan yana yiwa Jamiyyar APC waka ba za ka ji yana zagin wasu da ke cikin PDP kuru kuru ba. Da yawan lokaci mutum yake yiwa waka ba Jamiyya ba.

Misali a bana ya yiwa Janar Buhari waka ya kuma yiwa Ramalan Yero na Kaduna waka, a Jihar Yobe ya yiwa Sabo Garbu. Wannan ta nuna ba mawakin Jamiyya ba ne. Daga cikin dalilansa na rashin zage damtse ya zagi mutum a wakar Siyasa shine a gaba bai San irin juyin da siyasar za ta yi ba, kuma a duk Jamiyya ya San yana da Masoyan wakokinsa.
Idan Aminu Alanwaka zai yiwa Dan siyasa waka , ya San irin kalmomin da zai yi amfani da su, idan zai yiwa basarake waka yasan kalmomin da zai sanya a cikin wakar, sabanin wasu mawakan da za su yiwa sarki waka sai ka ji waka Kamar su na yiwa yan matan su, ko kuma irin wakar nan da ‘yan matan kauye ke yi musamman na Fulani idan Hatsi yayi kyau.

Ba kawai kaifin Basirar sa ne ke yiwa wakokinsa Ado ba, kaifin hange da nazari na karawa wakokinsa ado su na karbuwa ga Jama’a. Abin nufi duk abinda ya fadi mai saurare zai amince koda makiyi ne saboda gaskiya ya fadi. Wannan na daga cikin dalilan da ya sanya yanzu tsofaffi ba su da abubuwan saurare sai wakokinsa Aminu Alanwaka.
Kamar yadda na fadi banbancin a bayyane yake tsakaninsa da mawakan zamanin nan namu. Akwai wakar da yake rubutawa ta Sir Ahmadu Bello Sardauna,yau wajen shekara guda da rabi har yanzu bai kammala ba, a kalla littattafai sun kai biyar na turanci da Hausa Wanda yake Mazarin yadda Rayuwar Sardauna ta gudana har zuwa rasuwarsa. Akwai wakar da yake yi kan rayuwar fiyayyen halitta mai sunan MUHAMMADU MUFTHUL FUTUHATI LINZAMIN RAYUWA.
Waka ce da za ta yi bayani kan halayen Manzon tsira saw da dabiu da muamalarsa da alumna tarihinsa na haihuwa har zuwa wafatin sa SAW. Wakar yau kusan shekaru uku,amma bai fi baituka goma ba , don kawai nazari da bincike gami da tace irin kalmomin da ya dace yayi amfani da su. Ban San iyakar littattafan da yake nazari kan su ba.

Ni da shi mun sha zuwa gaban Malamai mu zauna akan wakar, domin tankade da rairayar gudun fadawa shubha. Wanda ke yin wannan dole ya zama yana da banbanci da Mawakan mu na yanzu wadanda da Dama daga cikin su ‘yan oya_oya ne. Da yawa akwai mawakan da ke kwatanta hakan yadda yake yi amma fa a cikin Dari da wuya a iya samun goma.

Na sha fadi cewa abinda ya zubar da Kimar mawakan wannan zamani shine , kaso saba”in cikin Dari na mawakan ba mawakan baiwa ba ne, mawaka ne na cin abinci.

Rubutawa : Auwal G Danbarno.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button