Monday, 5 June 2017
Zan amsa kiran Real Madrid - Hazard

Home Zan amsa kiran Real Madrid - Hazard
Ku Tura A Social Media

Dan wasan gefe na Chelsea Eden Hazard ya ce zai duba bukatar Real Madrid idan ta bukaci sayensa, amma kuma ya ce zai ci gaba da zama a Chelsea na karin shekaru masu yawa.
Akwai jita-jita mai karfi da ke danganta Hazard wanda ya ji rauni a idon sawunsa a lokacin atisaye a tawagar kasar Belgium, da Zakarun Turan.
Dan wasan na Belgium ya sheda wa jaridar Het Laatste Nieuws cewa; ''Dukkanninmu muna da buri. Zai iya kasancewa Spain, zai kuma iya kasancewa ci gaba da zama a Chelsea.''
''Amma dai ba abin da nake tunani ba ne a yanzu. Amma za ,u ga abin da zai faru.''
Real ta doke Juventus 4-1 ta dauki Kofin Zakarun Turai a karo na 12, wanda ya kasance na uku a cikin shekara hudu.
Hazard ya kara da cewa, idan har zan je Real Madrid, zan iya kasancewa a benci ni ma, saboda haka abin da nake duba wa kaina shi ne zabi na gari.
Dan wasan mai shekara 26, wanda ya koma Chelsea daga Lille a watan Yuni na 2012, ya taimaka wa Blues din ta dauki kofin Premier a kakar da aka kammala.
Da aka tambaye shi ko zai iya barin Chelsea, sai ya ce, a kwallon kafa ba ka san abin da zai faru ba, amma dai a yanzu ya ce ba wannan abu a ransa.
Ya kara da cewa shi har yanzu dan wasan Chelsea ne, yana da sauran shekara uku. Amma zai ga abin da zai kasance.
A game da ko Chelsea za ta bukaci ya tsawaita kwantiragin nasa, sai ya ce a yanzu dai kungiyar ba ta bukace shi da hakan ba, amma dai za ta iya ba shi.
Hazard ya ce a 'yan shekarun da suka gabata kowa yana maganar cewa zai koma PSG ne, a bana kuma Real Madrid ake cewa, shekara mai zuwa kuma wata kungiyar za a ce.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: