Saturday, 10 June 2017
Wasu Mutane Da Ba'a San Ko Su Waye Ba Sun Kone Wani Mutum A Garin Kura Dake Jihar Kano

Home Wasu Mutane Da Ba'a San Ko Su Waye Ba Sun Kone Wani Mutum A Garin Kura Dake Jihar Kano
Ku Tura A Social Media
Wasu Mutane Da Ba'a San Ko Su Waye Ba Sun Kone Wani Mutum A Garin Kura Dake Jihar Kano

A ranar Larabar da ta gabata ne da tsakar dare wasu da ba'asan ko su wane ba suka je karamar hukumar Kura dake jihar Kano da wannan bawan Allah a cikin mota a daure, daidai titin zuwa kauyen Bugau bayan Nitel suka tsaya suka fito dashi suka kone shi kurmus sukayi tafiyarsu.

Fulanin dake kusa da wajen sun shaida hakan, domin sune suka ankarar da abin dake faruwa, kafin ayi yunkurin daukar mataki har sun kone shi sun gudu.

Wayewar gari jami'an tsoro sunje sun tafi da gawar zuwa babban sashin bincike na hukumar 'Yan Sanda ta jiha. Sai dai ana kyauta zaton mutanen daga cikin birnin Kano suka fito da mutumin.

Allah ya tsaremu, ya tsare mana imaninmu.

Daga Shafin Hausa Daily

Share this


Author: verified_user

0 Comments: