Saturday, 10 June 2017
Tsagerun Niger Delta Sun Ba 'Yan Arewa Wa'adin Barin Yankin

Home Tsagerun Niger Delta Sun Ba 'Yan Arewa Wa'adin Barin Yankin
Ku Tura A Social Media
Gamayyar kungiyoyin Tsagerun Niger Delta sun baiwa 'yan Arewa da ke zaune yankin wa'adin watanni uku kan su fice daga yankin sannan kuma gwamnatin tarayya ta karbi rijiyoyin man da 'yan Arewa suka mallaka tare da mika su ga 'yan asalin yankin.

Kungiyoyin kuma sun yi ikirarin cewa a ranar 1 ga watan Oktoba za su bayyana 'yantacciyar kasarsu. Shugabannin kungiyoyin sun hada da; ‘General’ John Duku (Niger Delta Watchdogs and Convener: Coalition of Niger Delta Agitators), ‘General’ Ekpo Ekpo (Niger Delta Volunteers), ‘General’ Osarolor Nedam (Niger Delta Warriors), and ‘Major-Gen.’ Henry Okon Etete (Niger Delta Peoples Fighters), ‘Major-Gen.’ Asukwo Henshaw (Bakassi Freedom Fighters), ‘Major-Gen.’ Ibinabo Horsfall (Niger Delta Movement for Justice), ‘Major-Gen.’ Duke Emmanson (Niger Delta Fighters Network), da kuma ‘Major-Gen.’ Inibeghe Adams (Niger Delta Freedom Mandate).

Sources:Facebook/Rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: