Kannywood

Nafisa Abdullahi Ta kafa Sabon Tarihi a Kannywood

Shahararren kamfanin nan mai shirya fina-finan Hausa Abdul Amart Maikwashewa ya saki tirelan sabon fim din da ake ta jira mai suna SULTANA.

Sultana dai fim ne da ya kunshi Shahararru kuma jaruman ‘yan fim da ya hada da Jaruma Nafeesat Abdullahi.
Wannan fim dai anayi masa kirari da ‘dakamar ba a taba yin irinsa ba’ tun kafin ya fito ganin irin jaruman da suka fito a fim din.

Abdulamart ya saka wannan tirela ne a shafinsa na Instagram.

Jaruman da suka fito a fim din sun hada da Sarki Ali Nuhu, Wassh Waziri,Hauwa Maina, Adam Zango da dai sauransu.
Wasu daga cikin wadanda suka kalli tirelan sun yabi irin jarumtakar Nafeesat Abdullahi a fim.

Ameera Yunus ta zanta da gidan jaridar Premium Times Hausa inda ta ce Nafeesat ta kure jarumtaka a wannan fim din kuma ita hakurinta na neman ya gajarta wajen jiran fim din.

” Duk da Nafeesat jaruma ta ce da nafi so a farfajiyar fina-finan Hausa wannan karon ta kure ni din tirelan Sultan kawai ya gama dani. A gaskiya an ja mana rai da wannan tirela amma mana nan muna jira.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button