Sunday, 11 June 2017
Martani Ga Sarkin Katsina,kuma Kalubale Ga Dattawan Arewa!!!

Home Martani Ga Sarkin Katsina,kuma Kalubale Ga Dattawan Arewa!!!
Ku Tura A Social Media
MARTANI GA SARKIN KATSINA, KUMA KALUBALE GA DATTAWAN AREWA

DAGA: ALI MUHAMMD IDRIS (ARTWORK)

Lallai ne mu farka mu ci gaba da fahimtar wani aiki dake gabanmu mu talakawa. Ina bibiyar shafin RARIYA na ci karo da wasu batuttuka da suka yi taron dangin cusa min bacin rai da kuma mamaki mai girma. Mu dai mun san asalin Sarakunan mu, sarauta da rayukansu sun ginu ne akan taimakon talakawan arewa da kuma kiyaye martaba da kimar mu. Sarakuna suke tsayawa tsayin daka dan tabbatar da al’adu da dabi'u masu kyau na Arewa tare da zame mana murya mai amfanarwa.

Saidai kash! Wani bakon yanayi ya shiga cikin sarakunan mune? Shin a ina matsalar take ne? Menene ya kore dattako da kishin arewa a zukatan sarakunan mu? Shin sun hakura da mune sun rungumi 'yan kudu?

Sarkin Katsina yana fadin cewa “ZAI IYA BADA JININSA DAN 'YAN KUDU”.

Saidai ina da wasu tambayoyi da nake neman amsa, ina so talakawa irina na arewa mu taru mu nemi amsar a wurinsa.

Na farko, shin wane mataki Sarkin Katsina ya taba dauka da aka cutar da yan arewa a kudu, musamman rikicin ILE EFE? Idan bai dauki mataki ba, wane furuci ya yi da ya nuna yana kishin Arewa? Shin jininsa bai yi kama dana ‘yan arewa bane da bazai iya bada shi ga "yan arewa ba amma zai iya mika shi ga 'yan kudun?

Wace daraja ya taba samu a gun 'yan kudu sama dana arewa? Shin ko dai ba ta mu yake ba ta su yake yi? Shin ina martabar da ya kamata ya ba mu? Shin menene aikin Sarki ga talakawansa? 

Mufa ba fatan mu mu tada fitina ba, amma muna bukatar mu ga an yi adalci ga kowanne bangare. A bashi gaskiya da rashin gaskiyar sa. Kodai maganar da muke yi  tsakanin mu matasa haka take? Cewa dukkansu suna da kamfaninnika a kudanci ne ya sa basa son su yi magana a can koda wani abu ya faru da yan arewa dan kar a farma dukiyoyinsu dake can?

Mun san suna da hannun jari ne acan yasa mu a taba mu ba za su iya magana ba amma a yi kokarin taba su su dauki hukunci.

Me ya sa suka nuna sun fi mu kishin nasu? Saboda jim kadan da barazanar da aka yiwa ‘yan kudu (Igbo) wasu daga cikin gwamnonin su suka yunkuro domin tattaunawa su fitar da mafitar da za ta tseratar da nasu.

Kun ga bambanci ya fito fili, sun nuna sun fi daraja nasu sama da yadda namu suke daraja yan arewa, saboda mu a lokacin da aka halaka mutanen mu a ILE EFE. Me ya sa babu wani gwamna da ya yunkuro balle akai ga maganar taro dan kwato darajar yan arewa a can, in ka dauke mutum daya mai kishin arewa DR. RABIU MUSA KWANKWASO.

Idan Sarki ya bada amsa to za mu ci gaba da fahimtar alkibilarsa. Saidai ina ci gaba da tunatar da cewa, ban yi rubutu na da nufin tada zaune tsaye ba, ban kuma yi dan nuna rashin kunya ko rashin biyayya ba.
Ina dai tunatar da su ne ni dan arewa ne mai kishin arewa, mai son ganin ci gaban arewa. Dama Nijeriya baki daya, Mai son ganin shugabanin mu suna kwatowa yan arewa yanci da darajarsu. Mai yi wa shugaban kasa MUHAMMAD BUHARI fatan alkairi da fatan Allah ya kara masa lafiya mai dorewa dan ci gaba da mulkin mu bisa adalci.

Daga: ALI MUHAMMAD IDRIS (ARTWOK)

©Facebook /Rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: