Wednesday, 7 June 2017
Man United ta wuce Madrid arziki a duniya

Home Man United ta wuce Madrid arziki a duniya
Ku Tura A Social Media


Kungiyar Manchester United ta hau kan Real Madrid a matsayin wadda ta fi arziki a fagen tamaula, in ji mujallar Forbes.
United ta kai darajar fam biliyan 2.86, wanda hakan ya sa ta koma ta daya a duniya, matakin da ta rike a shekara biyar da ta wuce.
Barcelona ce ta biyu wadda ke da kadarar fam biliyan 2.82, sai Real Madrid wadda mujallar ta Forbes ta ce tana da kadarar fam biliyan 2.77.
Kungiyoyin Ingila guda shida ne suke cikin goman farko na kungiyoyin da suka fi arziki a duniya a jadawalin da mujallar ta fitar.
Ga jerin kungiyoyi 20 da suka fi arzikin a duniya:

1. Manchester United (£2.86bn)

2. Barcelona (£2.82bn)

3. Real Madrid (£2.77bn)

4. Bayern Munich (£2.1bn)

5. Manchester City (£1.61bn)

6. Arsenal (£1.5bn)

7. Chelsea (£1.43bn)

8. Liverpool (£1.15bn)

9. Juventus (£976m)

10. Tottenham (£821m)

11. Paris St-Germain (£652m)

12. Borussia Dortmund (£626m)

13. AC Milan (£621m)

14. Atletico Madrid (£567m)

15. West Ham (£491m)

16. Schalke 04 (£487m)

17. Roma (£441m)

18. Inter Milan (£416m)

19. Leicester City (£320m)

20. Napoli (£294m)

©bbchausa.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: