Thursday, 1 June 2017
Gwamnatin Tarayya Za Ta Bude Makarantu Na Musamman Saboda Matan Aure

Home Gwamnatin Tarayya Za Ta Bude Makarantu Na Musamman Saboda Matan Aure
Ku Tura A Social Media
Gwamnatin tarayya ta ce za ta bude makarantu na musamman saboda matan da aka cire daga makaranta saboda a yi masu aure.

Ministar harkokin mata Aisha Alhasan ita ta bayyana haka ga manema labarai a yau Alhamis a jahar Katsina, inda ta ce makarantun za su baiwa matan damar komawa makaranta daga gidajen mazajen su.

Ta ce za a bude makarantun a matakai guda biyu saboda kar a samu matsaloli.

Mataki na daya na wadanda suka bar makarantun sakandire ne kafin su kammala, mataki na biyu kuma na yaki da jahilci.

Ta bayyana cewa za a bude makarantun yaki da jahilcin a kowacce karamar hukuma a fadin kasar nan.

Haka kuma banda darusussuka da matan za su na dauka, za a koya masu sana’o’i kamar su dinki, hada man shafawa, sabulu, lemon sha, kyandir da sauran su.

Ministar ta yi kira ga malamai da shugabannin gargajiya da su baiwa gwamnati hadin kai wajen cimma manufofin ta na ilimantar da mata, saboda ya na da matukar muhimmanci.
Daure ka/ki yi sharhi:

Share this


Author: verified_user

0 Comments: