Wednesday, 14 June 2017
Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Dauki Nauyin Tura Malamai 90 Zuwa Umra Domin Yi Wa Shugaba Buhari Da Nijeriya Addu'a

Home Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Dauki Nauyin Tura Malamai 90 Zuwa Umra Domin Yi Wa Shugaba Buhari Da Nijeriya Addu'a
Ku Tura A Social Media
Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Dauki Nauyin Tura Malamai 90 Zuwa Umra Domin Yi Wa Shugaba Buhari Da Nijeriya Addu'a

Daga Aminu Dankaduna Amanawa

Gwamnatin jihar Sokoto karkashin ma'aikatar lamurran addini ta jihar ta dauki nauyin tura malaman addinin musulunci 90, domin gudanar da umrah a kasar Saudiyya.

Yayin da Malaman suke a Saudiyya za su gudanar da addu'oi na musamman domin samun lafiyar shugaba Buhari da cigaban jihar Sokoto da kasa baki daya.

An dai bawa malaman naira dubu 50 ko wannen su domin bukatocin iyalansu na gida, yayin da suke a kasa mai tsalki.

Malamman dai ana sa ran tashin su zuwa Saudiyya a gobe Laraba.

©Rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: