Thursday, 8 June 2017
Farashin Kayan Abinci Da Sauran Kayan Masarufi Za Su Fado Warwas-inji Ministan Noma

Home Farashin Kayan Abinci Da Sauran Kayan Masarufi Za Su Fado Warwas-inji Ministan Noma
Ku Tura A Social Media
Farashin Kayan Abinci Da Sauran Kayan Masarufi Za Su Fado Warwas Cikin Makonni Biyu Masu Zuwa, Inji Ministan Noma

Daga Haji Shehu

Ministan Noma, Audu Ogbeh, wanda shine ke shugabantar hukumar da fadar shugaban kasa ta kafa domin samar da sassauci kan farashin abinci a kasa ya tabbatar da cewar za'a samu sassaucin farashin kayayyakin abinci a cikin sati biyu masu zuwa.

Ogbeh yace wannan hasashe na zuwa ne bayan wani aikin sirri da komitin ya gabatar a kokarin gwamnatin tarayya na samarda wadataccen abinci cikin rahusa.

Mun tattauna da manoma don samun mafita kan yadda za'ayi farashin abinci ya ragu. Gwamnati ta fadada ayyukanta ta fuskoki mabanbanta don ganin ta karfafa harkar noma abinci ya wadatu.

Ministan ya cigaba da cewar " Nayi amanan cewar hauhawan farashin abinci abune maras kyau ga mutanen da ba manoma ba, amma abune mai kyau ga kasa kasancewar motane da yawa zasu koma noma. A karshe kuma za'a sami wadataccen abincin da zaisa farashi yayi faduwar dole"

Share this


Author: verified_user

0 Comments: