Dariya Zallah: Bafulatani Da Farfesa!!!

Farfesa ya ce idan nayi maka tambaya baka amsa ba zaka bani 5,000. Idan kuma kayi min tambaya bansaniba zan baka 20000.Profesa ya tambayi bafulatani “nawa ne nisan sama zuwa kasa?” Bafulatani ya ce bai sani ba.
Bafulatani ya ba da 5000.
Bafulatani ya ce saura ni.”Wace dabba ce idan tana kasa tana da kafa 4 idan ta soma tashi tana da kafa 3 idan tayi sama sai ta koma kafa 2 idan ta tashi saukowa sai ta sauko da kafa 1?” Farfesa ya zaro 25,000 dan bai sani ba. Bafulatani zai tafi sai profesa yace “menene ansar?”. sai bafulatani ya zaro 5,000 ya karawa profesa ya ce NIMA BAN SANI BA.
Hahahaha!!!! Duk da hakan sai ku ce Fullo bai da wayo.
Daure ka/ki yi sharhi

Share this


0 comments:

Post a Comment