Tuesday, 13 June 2017
Damfarar Naira Miliyan 29 A Sokoto: Iyalan Abdullahi Saka-Samu Milgoma Sun Nemi Kwamishinan Shari'a Da Cif Jojin Jiha Da Su Tsoma Baki

Home Damfarar Naira Miliyan 29 A Sokoto: Iyalan Abdullahi Saka-Samu Milgoma Sun Nemi Kwamishinan Shari'a Da Cif Jojin Jiha Da Su Tsoma Baki
Ku Tura A Social Media
Alh Abdullahi saka-samu Milgoma

Wasu 'yan uwa da abokan kasuwanci na Alhaji Abdullahi Saka-Samu Milgoma dan kasuwa da aka yi wa damfara ta makudan kudade har naira miliyan ishirin da tara da dari uku da tsamanin (29,380,000) a watanni baya da sunan kudin cinikin buhunan shinkafa da man gyada da yayi ciniki ta hannun wasu da ake zargin yan damfara ne na neman ceton Kwamishinan Shari'a na jahar Sokoto, Barrister Suleiman Usman da Cif Jojin Jaha Mai Shari'a Bello Abbas dangane da zargin nuna alamun rashin adalci ga yadda ake sauraren Shari'arsu a Kotun Kasuwa dake Sokoto.

Bayanin koken wanda Malam Ibrahim Tambuwal ya sanya wa hannu a madadin yan uwa da abokan hulda na Mai koken ya zargi cewar ana yunkurin amfani da wasu hanyoyi na dubarun Shari'a don baiwa wadanda ake zargin da samun wata hanya tserewa bayan duk binciken da akayi da bayanin da masu laifin suka yi sun amince da cewar, sune da kansu suka yi damfara kuma har sun gina gidaje da sayen motoci daga cikin kudaden da suka damfarari Alhaji Abdullahi Saka-Samu Milgoma na makudan kudaden jama'a. 

Malam Ibrahim Tambuwal yace wadanda ake zargin Faruku Dan Dubai Birnin Kebbi da Alh Sani Gwandu sun yiwa Alhaji Abdullahi Saka-Samu Milgoma yaudara ta fitar hankali tare da damfararsa ta 419 kusan watanni 4 da suka wuce  na karbar kudaden kamun ciniki har naira miliyan N29,380,000 daga cinikin da suka yi na sayar masa da shinkafa buhu dubu biyar da man gyada jalka dubu biyar da aka kiyasta sun tashi akan kudi naira miliyan dari da ishirin (N120,000 000) amma da suka karbi kudin a matsayin somin tabi na biyan kayayyakin sai suka yi ko kasa ko sama har tsawon watani ukku ana cigiya da wahalar nemansu babu bayani. 

Bayanin nasa ya zargi cewar, Faruk Dan Dubai ne ya zo a wurin Alhaji Abdu Milgoma da cewar, shine babban jami'in Kwastam, Watau Mataimakin AC (AC Comptroller Customs)  na Hukumar Kwastam dake kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara,  inda yace yana da shinkafa har dubu biyar da man Gyada jalka dubu biyar. 

Bayan kulla ciniki ta hannun yaron sa, Abubakar Nahantsi, watau Abu Dange wanda shine yayi masa rakiya sai wasu yaransa Aliyu Sabon Birni da Hassan Sani Suleja suka nemi a basu kudi amma Alhaji Abdullahi yaki da cewar sai har ya ga kayan.

Sakamakon irin damuwa da tabbacin da abokin huldarsa Abubakar Nahantsi (Abu Dange) ya bashi ya samu kwarin guiwa dangane da nemo cikon kudaden daga wasu abokan hulda da yan uwa don hada kudaden da zai bayar a matsayin kashi 1/3 na kudaden cinikin kayan. 

Alhaji Sani Gwandu ne ya karbi kudin bisa umurnin Faruk Dan Dubai  kamin su wuce Illela don dauko kaya, amma da akaje Illela babu kaya kuma Faruk Dan Dubai yaci layar zana ya bace.

Duk yunkurin da akayi na maido da kudin wadanda mallakar wasu yan kasuwa ne da suka yi karo karo don ciniki, abin yaci tura. Bayan kama su da gabatar dasu gaban yan sanda sun amince da yin damfara da karbar kudaden ga hannun Alhaji Abdullahi Milgoma har ma da kama motoci biyu da suka saya, sai kuma gidan da aka gina a GRA na Birnin Kebbi cikin kudin damfara, inji bayanin Ibrahim Tambuwal. 

Zuwa yanzu dai yan uwan na zargin akwai wata munakisa daga Kotun Kasuwa dake Sokoto wadda Mai Shari'a Fati Dewa take jagoranci na kokarin rashin adalci, inda baya ga bayar da belin yan damfara da akayi an hana musu shiga kotu don bayar da shaida akan wadanda ake zargi, mussaman ma wadanda shaidu ne. 

Koken na yan uwan Abdullahi Milgoma yayi mamakin yadda za a ci gaba da tsare masu shaida amma a bayar da belin wadanda ake zargin sun aikata laifi, duk kuwa da sanin cewar, hakan na da illa mai yawa ga shari'a ta gaskiya da adalci. 
Alh Ibrahim Tambuwal

Alhaji Ibrahim Tambuwal ya baiyana cewar, dasu da dan uwansu basu gamsu da yadda Mai Shari'a Fati Dewa take gudanar da wannan shari'a ba, sakamakon zargin cewar ba zata yi musu adalci ba ganin yadda wadanda ake zargin suka yi ma Abdullahi Milgoma barazana a gaban kotu tare da katsalandan ga ci gaban shari'a da ake gudanarwa. 

Don haka sun bukaci Kwamishinan Shari'a na jahar Sokoto da Cif Jojin Jaha da Hukumar Kula da Harakokin Shari'a na jahar Sokoto dasu binciki wannan matsalar tasu tare da dauke shari'a zuwa wata kotu saboda adalci da gaskiya akan wannan lamari. 
Yace hakika ko kadan hankalinsu bai kwanta da irin yadda take-taken da da Mai Shari'a Fati Dewa take amfani dasu wajen karba da sauraren bayanai na shaida ga wadanda akayi abin a idonsu ba. 

Kokarin jin ta bakin Mai Shari'a Fati Dewa ko wani na kusa da Kotun Majistare ta Kasuwa yaci tura, inda Mataimakiyar Rajistara akace bata fito aiki ba, saboda daya daga cikin ya'yyanta na fama da rashin lafiya.

©Rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: